Saturday, May 5, 2018

ZINARIYAR MAGANA.

ZINARIYAR MAGANA.

An tambayi Imam Hasanul Basariy (Rahimahullah), mene ne sirrin gudun-duniyarka?
Sai ya ce wasu abubuwa hudu ne:
1. * Na san cewa rabona ba wanda zai same shi, don haka hankalina yake a kwance.
2. * Na san cewa aikina ba mai yi sai ni, don haka sai na shagaltu da shi ni kadai.
3. * Na san Allah Ta'ala yana kallona, sai nake jin kunyar ya gan ni ina aikata laifi, sai na nisanci zunubi.
4. * Na san cewa mutuwa na jira na, don haka sai nake ta tanadin guzuri na kwarai don shirin gamuwa da Ubangijina.

Fatawoyin Azumi

FATAWOYIN AZUMI


 1. YA HALATTA IDAN MUTUM YA DAUKI AZUMIN RAMADANA DA SHAIDAR MUTUM DAYA?
Ya halatta, wannan shine Ra'ayin Abu hanifa da imamu shafi'i da imam Ahmad ibn hanbal, sannan wannan shine Ra'ayin ibni munzir.
Abu malik yace, koda mace ce ta bayar da shaidar taga watan Ramadana, to za'a karbi shaidarta kuma ayi aiki da wannan shaidar.
(Sahih fiqhussunnah 2/82-83)

2. IDAN MUTUM YAGA WATAN RAMADAN SHI KADAI YA BAYAR DA SHEDA BA'A YARDA BA, YA HALATTA SHI AKANSA YAYI AZUMI?
Anan Akwai maganganu guda ukku.
* zai dauki azumi sannan bazai sauke ba, har sai tare da mutane.
Wannan shine Ra'ayin Abu hanifa da Imam maliku ibn Anas.
*baxai dauki azumi ba, sai mutane sun dauka, sannan ya sauke tare da mutane.
Wannan shine shine Ra'ayin Imam Ahmad ibn hambal, Sannan wannan shine zabin Shaikul Islam ibni Taimiyya.
*zaiyi Azumi sannan zai sauke ba tare da mutane sun sani ba, sabida kar ya zama ya sabawa jama'ah. Sabida sabani sharri ne inji Abdullahi dan mas'ud.
Wannan shine Ra'ayin Imam Ahmad da Da ibni Hazmin. (Sahihu fiqhussunnah, 3/82-83).

3. IDAN MUTANEN WANI GARI SUKAGA WATA, SHIN AZUMI YA HAU KAN MUTANEN WANNAN GARIN NE KO KUWA YA HAU KAN KOWA DA KOWA?
Idan mutanen wani gari sukaga watan Ramada, ya zama wajibi akan sauran garuruwa su dauki azumi.
Wannan shine Ra'ayin Abu hanifa da imamu maliku da wani bangare na imamushshafi'i, sannan wannan shine Ra'ayin Abu hanifa. (Sharhul kabeer 1/510, majmu'u fatawa 6/273, Al-insaf 3/273).

4. IDAN MUTUM YA SHA RUWA KO YACI ABINCI YANA TUNANINSA RANA TA FADA, SAI DAGA BAYA YAGA ASHE RANA BATA FADI BA, YAYA AZUMINSA?
Azuminsa yana nan kuma babu ramuwa akansa.
Wannan shine Ra'ayin imam Ahmad ibn hambal da imamu shafi'i da Dawud da Ibni hazmin da Ibni Taimiyya, sannan wannan shine ra'ayin da yawa daga cikin magabata na kwarai. (Almuhalla 6/220, majmu'u Fatawa 25/231.)

5. IDAN MUTUM YA SADU DA MATARSA A WATAN RAMADANA, GABAKI DAYANSU NE ZASUYI KAFFARA, KO KUMA MIJIN NE KADAI ZAIYI KAFFARA?
Babu kaffara akan wannan matar, kaffara akan mijin take kawai.
Wannan shine Ra'ayin Imamu shafi'i da Imam Ahmad ibni Hambal.
Hujjarsu, hadisin Abi huraira, wanda Muslim ya fitar dashi lambar hadisi na (1111).
wani mutum yazo wurin manzon Allah saw yace, ya manzon Allah, na Afkawa matata a watan Ramadan, sai manzon Allah saw yayi masa umarni da yayi kaffara shi kadai, ba tare sa ya umarci matarsa da tayi kaffara ba.
Abu malik A cikin sahihu fiqhussunnah yace, idan har wannnan matar bataso ne mijin ya nemeta, ko ta manta da cewar Azumi takeyi ko kuma jahila ce, to babu kaffara akanta.
Kenen idan tana so ne, kuma tasan haramun ne, to akwai kaffara akanta itama.

Allah shine masani

Zan Iya Rama Azumina a Litinin da Alhamis tare da Sittu?

Assalamu alaikum malam tambayana shine ina rama azumina a litinin da alhamis yayi? Amma fa nayi sittu?

Wa alaikum as salam,an yı sabani game da yın sittu shawwal kafin a gama ramuwar Ramadan, zance mafi inganci shi ne : ba za'a yi ba, saboda Annabi (s.a.w)a hadisin Müslim ya sanya ladan sittu shawwal ne bayan kammala Ramadan.
Za ki iya rama azumin Ramdhana ranar litinin da alhamis, saidai ba za ki samu ladan su gaba daya ba, saboda manufar su ta banbanta, saboda ko da ace ibadoji Iri daya ne, in manufar şu ta banbanta kowacce za ta ci gashin kanta, wata ba za ta wakilci 'yar'uwarta ba.
Allah ne mafi Sani.